Gwamnatin Sokoto Ta Ce Ba Zata Yi Sulhu Da Turji Ba Har Sai Ya Sako Mutanen Da Ya Sace
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi. Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne […]




