An Naɗa Tsohon Babban Hafsan Sojin Ruwan Nijeriya Gwamnan Riƙon Ribas 

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakinsa da daukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar.

Tinubu ya kuma ayyana Navy Vice Marshal Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin Gwamnan Rikon Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya game da harin da aka kai wa bututun man fetur a Jihar.

“Ina amfani da tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya wajen ayyana dokar ta-baci da kuma dakatar da gwamnan da mataimakinsa da zabbabbun ’yan majalisar na tsawon wata shida, daga yau 18 ga watan Maris, 2025” in ji shugaban kasan.

Ya sanar da hakan ne jim kadan bayan shan ruwa a ranar Talata, ’yan sa’o’i bayan wani zaman gaggawa da ya yi da manyan hafsoshin tsaro a sakamakon harin da ’yan ta’adda suka kai kan bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP) da ke yankin Bodo da ke Karamar Hukumar Gokana ta Jihar Ribas.

Mahara sun kai harin ne bayan barazanar yin hakan da suka bayar a makon jiya a sakamakon kara tsanani da rikicin shugaban jihar ya yi tsakanin ’yan majalisar da kuma gwamna Simi Fubara.

Ibok-Ete Ibas shi ne tsohon Babban Hafsan Sojin Ruwa na Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2021 a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda