An Rushe Hukumar Zaɓen Burkina Faso 

Gwamnatin Burkina Faso ta rushe hukumar zaben kasar, ta ayyana ta a matsayin almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a. 

Gwamnatin sojin ƙarƙashin jagorancin kyaftin Ibrahim Traoré ta ɗora wa ma’aikatar harkokin cikin gida nauyin gudanar da zaɓe.

Wannan na ƙunshe a cikin wani labari da gidan talabijin na RTB na gwamnatin ƙasar ya ruwaito.

Tun bayan kwace mulki a watan Satumban 2022, Gwamnatin sojin ta fara gudanar da gagaruman sauye-sauye, ciki har da ɗage zaben da zai kai ga komawar ƙasar turbar dimokuraɗiyya.

A shekarar da ta gabata ne dai ya kamata a yi zaɓe a fadin kasar, amma gwamnatin mulkin sojan ta tsawaita wa’adin mika mulki ga farar hula har zuwa watan Yulin shekarar 2029.

Wannan twaita lokacin mayar da mulki ga farar hula ya baiwa shugaban gwamnatin sojin da ke ci a halin yanzu wato kyaftin Ibrahim Traoré damar ci gaba da juya akalar ƙasar da kuma ‘yancin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Post masu alaƙa

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC

DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja