Ana sace wani jariri sabuwar haihuwa ,a hannun mahaifiyarsa a yankin unguwar Kadwani marabar Gurku, dake ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa.
Lamarin faru ne ranar asabar ɗin data gabata, da ƙarfe 11:00pm, a kauyen dake da tazarar kilomita 18 da fadar shugaban ƙasa a Abuja.
Mahaifiyar jaririn mai suna, A’isha ta bayyana cewa, tana yin barci sai taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofa, kuma bayan ta haska fitila sai taga mutane biyu sun shigo da ƙarfi, sannan suka shaƙe mata wuya da rufe bakin ta tare da ƙwace jaririn.
Ta ƙara da cewa ta nemi taimakon jama’a lokacin da batagarin suka ƙwaci jaririn, kafin su gudu dashi amma bata samu ba, sakamakon mijin ta yayi tafiya zuwa jihar Lagos.
Mai unguwar Baƙo, Chief Abubakar Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka sanarwa da jami’an ƴan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don kamo waɗanda ake zargin.
Wani maƙocin wajen da lamarin ya faru,ya ce sai bayan da ɓarayin jaririn suka gudu sannan suka ji ihun matar, kuma ba wannan ne karon farko ba da aka samu labarin satar yara a yankin , inda suka nemi ɗaukin hukumomi da su samar mu su da ofishin ƴan sanda.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, SP Rahman Nansel, ya shaida cewa zai bincika domin bashi da masaniya kan abunda ya faru.