NOA ta ƙaddamar da manhajar ClheeanMobile App don ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnati da jama’a

Hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar waya mai suna CLHEEAN Mobile App, wadda aka tsara domin ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnati da al’umma tare da rage gibi a harkokin mulki.

Daraktan Janar na hukumar, Malam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa manhajar za ta bai wa ‘yan Najeriya damar samun bayanai kan manufofin gwamnati, ilimin zamantakewa da na ƙasa, tare da ba su damar isar da ra’ayoyinsu da koke-kokensu kai tsaye ga gwamnati.

Manhajar na ɗauke da (AI) mai amfani da murya da rubutu, tare da damar amfani da harsuna dabam-daban da suka haɗa da Hausa, Yoruba da Igbo domin sauƙaƙa sadarwa ga kowa.

Haka kuma, tana ba da damar bayar da rahoto kan matsaloli, shiga tattaunawa da muhawara, da kuma samun sabbin bayanai cikin sauri.

Hukumar ta buƙaci dukkan ‘yan Najeriya da su sauke manhajar domin su ba da tasu gudummawa wajen gina ƙasa.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda