Sarkin Haɗejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON ya tabbatar da Alhaji Mohammed Babandede matsayin Magajin Rafin Haɗejia kuma ɗan majalisar Sarki.
Alhaji Mohammed Babandede ya gaji mahaifinsa Alhaji Muhammad Babandede Sarkiki da Allah ya yi wa rasuwa a watan Nuwambar shekarar 2023.
Sabon Magajin Rafin ya karɓi takardar wannan hakimici ne a ranar Lahadi 15 ga Satumbar shekarar 2024 a gidansu da ke G.R.A Haɗejia.
Yayan sabon Magajin Rafin, tsohon shugaban Hukumar Shigi Da Fici ta Najeriya Muhammad Babandede OFR, OCM ya jinjinawa Sarkin Haɗejia bisa wannan karamci na tabbatar da ƙanin nasa a matsayin Magajin Rafin Haɗejia.
Sabon Hakimin ya godewa Sarkin Haɗejia bisa tabbatar musu da tarihin gidansu.
Ya ce “ Na godewa Allah da ya baiwa Sarkin mu, babanmu shugaban mu Alhaji Adamu Abubakar Maje CON damar tabbatar mana da wannan matsayi, muna roƙon Allah ya bamu ikon sauke nauyin da muka ɗauka, Allah ya iya mana kuma ya gafartawa mahaifin mu”.
Taron karɓar takardar tabbatar da wannan hakimici ya haɗo jama’a daga wurare da dama a Najeriya.