An Yi Haniya A Zauren Majalisar Dattawa Lokacin Tantance Christoper Musa

Majalisar Dattawan Najeriya ta shiga hayaniya yayin aikin tantance tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher  Musa a matsayin sabon ministan tsaro lokacin da wasu suka nemi ya rusuna ya wuce kawai ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba.

Sanata Sani Musa (jihar Neja) ne ya shawarci majalisar ta bari janar ɗin ya wuce kawai bayan ya amsa ‘yan wasu tambayoyi marasa yawa.

Sai dai waɗanda ke adawa da hakan sun haƙiƙance cewa dole ne sai an yi masa tambayoyi masu tsauri, abin da ya jawo hatsaniya tsakanin ‘yanmajalisar.

Bayan tsawon lokaci ana hauragiya, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya miƙe tsaye, wanda ke alamta neman kowa ya shiga taitayinsa bisa dokokin majalisar.

Da yake amsa tambayoyin, Christopher Musa ya bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya, kuma ya yi kira da aka kara himma wajen aiki da shirin kare makarantu na Safe School Initiative.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya