GOMBE

Kotu ta soke nasarar ɗan takarar ADC a Majalisar Wakilai

Babbar Kotun Tarayya mai lamba biyu da ke Gombe ta soke zaɓen Bashir Abdullahi Gaddafi a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar ADC mai neman kujerar Akko a Majalisar Wakilan Tarayya a zaɓen 2027. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Vera E. Ibrahim, ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gudanar da sabon […]

Read more

Gwamnatin Tarayya za ta biya tsofaffin ma’aikatan da ta sallama shekaru 20 da suka gabata

Gwamnatin Tarayya ta fara tantancewar ƙarshe domin biyan tsofaffin ma’aikatan da aka sallama daga aiki kusan shekaru 20 da suka gabata, bayan wasu daga cikinsu sun yi fama da rashin samun cikakkun haƙƙoƙinsu na tsawon lokaci. Daraktan-Janar na Ofishin Sauye-sauyen Ayyukan Gwamnati (BPSR), Dasuki Arabi Ibrahim, ne ya bayyana hakan a Gombe yayin da yake […]

Read more

Ɗan Majalisar Tarayya Yaya Tongo ya rasu

Ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye a Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo, ya rasu a ranar Juma’a a Abuja bayan doguwar jinya. Marigayi Yaya Bauchi Tongo, jigo ne a jam’iyyar APC wanda Gwamna Muhammad Inuwa ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Jihar Gombe da ma kasa baki ɗaya. Rasuwarsa ta zo ne […]

Read more

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence  (NSCDC) reshen jihar Gombe, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a ƙungiyoyin satar babura da na’urorin lantarki a sassa daban-daban na jihar. Kamen ya biyo bayan wasu samame da jami’an hukumar suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙananan hukumomin Billiri da Balanga da Akko […]

Read more

Danjuma Goje ya yi fatali da maslaha a Gombe ta Tsakiya

Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya yi fatali da tsarin maslaha da Jam’iyyar APC ta Jihar Gombe ta bi wajen tsayar da ’yan takara, yana mai cewa matakin ya saɓa da dokokin zaɓe da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyya. Wannan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar […]

Read more