Ana Zargin Yan Sanda Da Halaka limami Ta Hanyar Duka A Kano

Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga  jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda.

An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba.

An zarge shi da siyan buhun fulawa, wadda aka ce an sace a bara.

Mahaifinsa, Sheikh Adam Usman, ya bayyana cewa bidiyon na’urar CCTV ya nuna yadda jami’an ’yan sanda biyu suka yi wa ɗansa dukan tsiya a lokacin da suka zo su kama shi.

Ya ƙara da cewa an ci gaba da dukansa a ofishin ’yan sanda, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Sheikh Usman, ya ce wani abokin Salim ya bi jami’an zuwa ofishin ’yan sanda, sannan daga baya ya sanar da shi abin da ke faruwa.

Ya ce ya garzaya ofishin a daren da aka kama shi, amma aka hana shi ganin ɗansa, aka ce ya dawo washegari.

“Da na koma washegari, suka ce min ɗana ya yi rashin lafiya a daren da ya gabata aka kai shi asibiti. Amma daga baya na gano cewa tuni ya rasu.

“Da farko, an kai gawarsa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad a matsayin gawar ‘wanda ba a sani ba,’ amma aka ƙi karɓa.

“Sai aka kai shi Asibitin Ƙwararru na Abdullahi Wase, inda aka ajiye shi a ɗakin ajiye gawarwaki,” in ji mahaifin matashin limamin.

Ya cw tuni suka kai ƙara hukumar ’yan sanda, kuma an shaida musu cewa an kama wasu jami’ai bisa rashin ƙwarewa a aikinsu, ana kuma gudanar da bincike.

An bayar da gawar Salim a ranar 26 ga watan Satumba, domin a binne shi bayan kotu ta bayar da umarnin a yi gwaji a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Sakamakon gwajin zai fito cikin makonni huɗu.

Mutanen unguwar sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai sauƙin kai da son zaman lafiya, inda suka ce mutuwarsa ta jefa su cikin  damuwa.

Ƙoƙarin samun jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Post masu alaƙa

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Galadima ya rasu

Hadejia ta cika shekaru 120 da cin nasara kan turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.