Home » Anya Gwamnati Najeriya za ta iya kula da shirin yaƙi da cutar HIV

Anya Gwamnati Najeriya za ta iya kula da shirin yaƙi da cutar HIV

Najeriya ta yi ta fama wajen ɗaukar nauyin ɓangaren lafiya. Sai dai ƙasar nan ta gaza cika alƙawarin da ta ɗauka a shekarar 2001 a Abuja a yayin taron ƙungiyar raya ƙasashen Afirka da ya ayyana buƙatar ƙasashenta su ware kaso 15% ga ɓangaren lafiya a kasafin kuɗinsu na kowacce shekara. Sai dai kaso 5% Najeriya ke iya warewa fannin lafiyar

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Na tsawon shekaru, Najeriya ta yi ta fama wajen ɗaukar nauyin ɓangaren lafiya. Sai dai ƙasar nan ta gaza cika alƙawarin da ta ɗauka a shekarar 2001 a Abuja a yayin taron ƙungiyar raya ƙasashen Afirka da ya ayyana buƙatar ƙasashenta su ware kaso 15% ga ɓangaren lafiya a kasafin kuɗinsu na kowacce shekara. Sai dai kaso 5% Najeriya ke iya warewa fannin lafiyar.

Ko da a shekarar 2024, shekarar da aka fi bai wa fannin lafiya kasafi mai tsoka, an bai wa hukumar ne kaso 5.75% na kasafin kuɗin Najeriya.

Kuma mafi yawan kason kuɗin an ware ne domin biyan albashi da gudanarwar a maimakon magance cutattuka.
A shekarar goma 11 da ta wuce, kaso 72% aka kashe wa wajen biyan albashi a yayin da ɓangare kamar na cutar HIV ke cigaba da fuskantar ƙalubale.

Kasafin kuɗin yaƙin da cutar HIV shi ne koma baya domin mafi girman kason kuɗin gudanar da shirin na zuwa ne daga tallafin ƙasashen ƙetare.

Shugaban Amurka, Donald Trump, A watan Janairun 2024, ya dakatar da tallafin gaggawa na fadar shugaban ƙasar kwanaki 90 wanda ya haifar da damuwa a tsakanin jami’an lafiya da ƙungiyoyi na duniya.

A yayin da wannan mataki ya girgirza mutane da dama, shugaba Trump ya cigaba da nanata cewa matakin da ya ɗauka shi ne na fifita muradan Amurka da sama da ba wa ƙasashen waje tallafi.

Ga ƙasashe masu tasowa musamman ga ƙasashen Afirka da ke yankin sahara waɗanda suka fi cin gajiyar shirin na PEPFAR. Sai dai wannan mataki ya sanya damuwa game da makomar tallafin HIV.

Bayan kwanaki da bayyana matakin da shugaba Trump ya ɗauka, gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na ƙarfafa matakan ba da tallafi ga masu cutar HIV a cikin gida.
Wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta ɗauka bai canja ba duk da cewa gwamnatin Amurka ta ɗan sassauta kan wannan mataki na dakatar da tallafin.

Hukumar kula da masu cutar AIDS (NACA) ta sanar da shirin samar da kayan magunguna na cikin gida da ya haɗa da kayan gwaji da kuma magungunan da ake kira da ‘antiretroviral drugs’.

Duk da wannan mataki ne mai kyau, amma masana harkar lafiya sun nuna damuwarsu game da ɗorewar zuba kuɗi wajen kula da shirin a Najeriya.

A ranar 3 ga watan Fabarairu ne, majalisar gudanarwa Najeriya (FEC) ta amince da kashe Dala biliyan 1.07 wajen ɗaukar nauyin ɓangaren lafiya a ƙarƙashin shirin gina ɗan’adam da samar da daidaito (HOPE).

Sannan majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 4.8 wajen magance cutar HIV kamar yadda ministan kuɗi da kula da tattalin arziƙi, Wale Edun.

A ƙoƙarin gwamnati na cike giɓi a fannin lafiya, majalisar dattawa ta amince da kashe Naira biliyan 300 a cikin kasafin kuɗi na 2025.

Sannan akwai ƙarin Dala miliyan 200 da aka ware wa masu fama da cutar tarin fuka da HIV da da maleriya da foliya.

Bayanai daga shafin gwamnatin Amurka ya nuna cewa a tsakanin shekarun 2015 da 2024, Amurka ta baya da Dala biliyan 2.28 (Naira tiriliyan 3.4 a kan canjin kowacce Dala a 1,493 per) wajen taimaka wa Najeriya.

Wannan kuɗi daidai yake da kaso 53.21% na ɗaukacin kasafin kuɗin da Najeriya ta ware daga shekarar 2015 zuwa 2024.

A shekarar 2015, Najeriya ta karɓi, Naira biliyan 292.63 na tallafin HIV/AID wanda kuɗin ya ƙaru zuwa Naira biliyan 392.66 a shekarar 2016 da Naira biliyan 358.32 a shekarar 2017. wanna tallafi ya cigaba da inda Najeriya ta karɓi Naira biliyan 346.38 a shekarar 2018 da Naira biliyan 262.77 a shekarar 2019 da mafi yawan adadin wannan tallafi a na Naira biliyan 409.08 a shekarar 2020.

A shekarar 2021, Najeriya ta karɓi Naira biliyan 306.07 da Naira biliyan 370.26 a 2022 da Naira biliyan 341.90 a 2023 da Naira biliyan 328.46 a 2024.

Idan aka kwatanta da kasafin da Najeriya ta ware wa NACA za a ga cewa ya sha saɓatta juyatta a cikin waɗannan shekaru.

A 2015, cibiyar ta samu Naira biliyan 2.78 wanda ya ƙaru zuwa Naira biliyan 3.42 a 2016. Sai dai wannan ya ragu matuƙa zuwa Naira miliyan 738.49 a shekarar 2017.

Sai dai a shekarar 2018 kuɗin da ake bai wa cibiyar NACA ya ƙau zuwa Naira biliyan 4.53 da Naira biliyan 6.70 a 2019. Sai kuma kuɗin ya sake raguwa kaɗan zuwa Naira biliyan 6.21 a 2020 kafin a sakr ƙara wannan kuɗi zuwa Naira biliyan 4.51 a 2021.

Haka kuma a 2022, an bai wa cibiyar Naira biliyan 6.42 da Naira biliyan 8.28 a 2023. Zuwa shekarar 2024 kuɗin ya kai Naira biliyan 10.04, Sannan a 2025, an ware Naira biliyan 19.03 wanda shi ne kado mafi girma da aka taɓa warewa.

Sosai dai duk da haka, Najeriya na buƙatar ƙarin kuɗi kuma ya zama mai ɗorewa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?