APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano

Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano.

Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta samu rahotannin da suka tabbatar an samu rikici a Shanono, Bagwai da Ghari.

Ta ƙara da cewa masu kaɗa ƙuri’a sun tsere daga rumfunan zaɓe sakamakon tashin hankali, yayin da jami’an tsaro suka kasa shawo kan lamarin.

“APC na kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta soke zaɓukan cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma zaɓen mazaɓar Ghari a Jihar Kano saboda tashin hankali da kuma tada hargitsin ’yan daba da aka samu.

“’Yan daba ɗauke da makamai sun tarwatsa rumfunan zaɓe da dama,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa barin zaɓukan su ci gaba da gudana ya saɓa wa tsarin gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, kuma hakan zai iya zama barazana ga zaɓuka a gaba.

 

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara

Gwamnonin Najeriya na duba yiwuwar mayar da mafi karancin albashi N100,000

Rundunar ƴan sandan Kano ta yaba da zaman lafiyar da aka samu lokacin bikin babbar sallah