Daga : Shareep Khaleepha
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bar jam’iyyar PDP.
Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya sake jaddada goyon bayansa ga hadakar jam’iyyun siyasa don kayar da jam’iyyar APC a 2027.
Daily Trust ta rawaito cewa, a baya-bayan nan, rahotanni daban-daban sun nuna cewa Atiku yana tunanin barin PDP don shirin takarar shugaban kasa a 2027.
- Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yanke kan wani mutum
- Za A Yi Sabbin Manyan Makarantu 5 A Zaria A 2025 – Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
Rahotannin sun ce yana shirin komawa jam’iyyar SDP.
Amma a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar na nan a matsayin cikakken mamba na PDP.