Home » Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yanke kan wani mutum

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yanke kan wani mutum

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment
Rundunar 'yan sanda na shirin janye jami'anta masu yi wa manyan mutane rakiya da tsaro

 

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Edo, ta kama wani matashi mai suna Aireebiuwa dan shekaru 27 bisa samunsa da laifin yanke kan mutum sannan ya sanya a cikin wata Jaka.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, Moses Yamu, ya ce jami’ansu dake aiki a Evbuotubu tare da hadin gwiwar yan Banga ne suka samu nasarar kama wanda ake zargin.

Rahotanni na cewa an kama shi a ranar 7 ga watan Maris 2025 akan titin Igbinudu, karamar hukumar Oredo ta jihar.

Moses Yamu , ya kara da cewa lokacin da ake yiwa wanda ake zargin tambayoyi ya kasa bayar da gamshasshen bayani, lokacin da ake bincike akansa har ya tabbatar da cewa kan wani mutum ne da ya sare masa kai sannan ya jefar da gawarsa a kusa da, Ewaka Shopping Plaza.

wani dan uwan marigayin ya bayyana wa yan sanda cewa, gawar dan uwan sa ce mai suna Edobor Lawrence, mai shekaru 43.

Kwamishinan yan sandan jihar BettRundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Edo, ta kama wani matashi mai suna Aireebiuwa dan shekaru 27 bisa samunsa da laifin yanke kan mutum sannan ya sanya a cikin wata Jaka.

Kakakin rundunarey Otimenyin ya jajantawa iyalan marigayin tare da bada tabbacin cewa rundunar ba zata bar wannan abu da wasa ba , domin da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da shi a gaban kotu.

A karshe kwamishinan yan sandan ya shawarci matashi , su daina neman sai sun yi kudi ta kowacce hanya, domin hakan wata hanya ce da wasu ke fakewa da ita don aikata laifuka.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?