Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Tajudeen Abbas ya ce mazaɓarsa ta Zariya za ta samu ƙarin manyan makarantu gwamnatin tarayya biyar da na sakandire biyu a kasafin kuɗin 2025.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya ruwaito kakakin majalisar na bayyana a haka a lokacin liyafar buɗe-baki da Hon. Tajudeen ya shirya tare da al’ummar mazaɓarsa a ranar Asabar.
Ya ce matakin yunƙuri ne na ƙarfafa kambin Zariya a matsayinta na cibiyar ilimi mai zurfi.
Kakakin Majalisar ya ce sabbin makarantun da mazaɓar tasa za ta samu sun haɗa da Kwalejin Ayyukan Noma ta Tarayya da Makarantar Kula da Kiwon Dabbobi da Baye ta Tarayya da Kwalejin Fasaha ta Tarayya.
Sauran sun haɗa da Cibiyar Horas da Ayyukan Cigaba da Cibiyar Tattara Fasahohi da makarantar Masu Buƙata ta Musamman – wadda ta ƙunshi furamare da sakandire, da kuma Sakandiren gwamnatin Tarayya, kmar yadda NAN ya ruwaito.