Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƙasar ta tsallake wani muhimmin mataki a sauye-sauyen tattalin arzikinta, kuma yanzu tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.
Bayanin na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar.
Shettima ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako na zahiri, inda ya bayar da misali da ƙaruwar ajiyar kuɗin ƙasashen waje zuwa sama da dala biliyan 55, da ingantuwar kasuwar musayar kuɗaɗen waje, da kuma ƙaruwar tattalin arzikin ƙasar da kashi 4.45 cikin 100 a rubu’i na biyu na bana.
Mataimakin Shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin wata ganawa da ’yan Najeriya mazauna Amurka a New York, a wai ɓangare na babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Ya shaida wa mahalarta taron cewa duk da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, gwamnatin Tinubu na aiki domin sake fasalin tattalin arzikin ƙasar, musamman a fannonin ilimi da lafiya da kimiyya da fasaha da kuma noma, tare da samar da yanayin da zai jawo masu zuba jari.
Sanarwar ta ruwaito Shettima na cewa “Ku kwantar da hankalinku cewa duk da munanan labaran da kuke ji da gani a kafafen sada zumunta, ƙofar Najeriya a buɗe take domin kasuwanci. Mun tsallake wani muhimmin mataki, kuma muna kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.”
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su taka rawar gani wajen ci gaban ƙasar, yana mai bayyana ilimi da ƙwarewa da basirar da suke da ita a matsayin muhimman kadarori ga yunƙurin Najeriya na sauya fasalin tattalin arzikinta.