Mujahid Wada Guringawa

Kotu ta ba da belin El Rufai kan naira miliyan 100

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El Rufai. An bayar da belinsa ne kan naira miliyan 100 da mutum guda da zai tsaya masa kan makamancin kuɗin. Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana tsauraran ƙa’idodin belin inda ta ce wanda zai tsaya masa dole ne […]

Read more

Sanata ya bar APC a jajibirin zaɓen fidda gwani a Kebbi 

Sanatan Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC. A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban APC na mazaɓar Rafin Zuru mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Mayu, 2026, Sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar. […]

Read more

An kama ɓarauniyar jariri a asibiti a Zamfara.

An kama wata matashiya ’yar shekara 27, kan zargin satar jariri mai kwana 10 da haihuwa a Babban Asibitin Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Dubun wadda ake zargin ya cika ne kwanan da sace jaririn, inda ’yan sanda suka fara gudanar da bincike bayan samun rahoton. Bayanan samun ƙorafin ne Babban Ofishin ’Yan Sanda […]

Read more

Yusuf Buhari ya lashe zaɓen takarar majalisar tarayya a APC

Yusuf Buhari, ɗan tsohon shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari, ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaɓe na mazabar, Lawan Garba, ya ce Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 17,342, inda ya doke abokin takararsa, Auwalu Musa Daura, wanda ya samu ƙuri’u […]

Read more

Man City ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea 1-0

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin FA na shekarar 2026 bayan doke Chelsea 1-0. Antoine Semenyo ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Man City nasara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Wannan ne kofi na biyu da ƙungiyar ta lashe a kakar wasa ta bana bayan lashe kofin Carabao […]

Read more