KACRAN ya ti watsi da ƙirƙiro ƴansandan jihohi a Najeriya

Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kullen Allah ta yi kira ga hukumomin Najeriya su dakatar da batun ƙirƙiro ƴansandan jihohi a faɗin ƙasar.

Yayin tattaunawarsa da BBC, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mohammed Khalil Bello ya ce shirin ba shi da wata fa’ida illa haifar da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.

Ƙungiyar makiyayan ta bayyana fargabar cewa wasu jihohin za su yi amfani da ƴansandan jihohin wajen musguna wa mambobinta.

”Muna fargabar wasu gwamnonin za su yi amfani da ƴansandan wajen ƙuntata wa wasu al’ummomi da ba sa so”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Shugaban na Kullen Allah ya kuma ce jihohin ba za su iya ɗaukar ɗawainiyar yansandan ba, don haka wahalhalu ne kawai za su ƙarar wa al’ummomin johohi musamman ma’aikata da yanfansho a cewarsa.

”In ka cire jihar Legas da jihohi masu arzikin man fetur babu jihar da za ta iya ɗaukar ɗawainiyar rundunar ƴansandan jiharta, don haka wannan ƙarin wahala ne ga jihar”, kamar yadda ya bayyana.

Ya kuma ce idan har aka yi yansandan jihohi, to gwamnoni za su daina bai wa sojoji da ƴan sakai tallafin da suke buƙata domin magance matsalolin tsaron jihohin.

Daga ƙarshe ya yi kira ga hukumomi maimakon ƙiriƙiro yansandan jihohi, gwamnatin tarayya ta ƙara yawan jami’an tsaron da take da su a yanzu tare da inganta musu albashinsu.

Haka kuma ya sake kiran a yi amfani da hanyar tattaunawa da kuma afuwa da samar da ayyukan yi ga matasa wajen magance matsalar tsaron da arewacin ƙasar ke fama da ita.

Post masu alaƙa

An kama wasu mutum 7 da ake zargin ƙusoshin Boko-Haram ne a filin jirgin Katsina

INEC na shirin cire NDC daga rajistar jam’iyyun siyasa bayan hukuncin kotu

Za a samu katsewar lantarki a Kano da wasu jihohin Arewa ranar Lahadi