Mujahid Wada Guringawa

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwato nau’in ƙwayoyi daban-daban har guda 5,916 da kuma kunshin tabar wiwi guda biyar. Kamen dai ya biyo bayan wasu samame na musamman da rundunar ta gudanar bisa bayanan sirri a wurare daban-daban na jihar, domin […]

Read more

Ebola ta ƙara bazuwa a DR Congo

Jami’ai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce barkewar cutar Ebola ta bazu zuwa wani lardi, wanda shi ne na bakwai. Gwamnan Sud-Ubangi ya ce an tabbatar da samun cutar a yankin da ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Kongo. An yi imanin cewa majinyacin ya bi ta wasu larduna da dama, ciki […]

Read more

Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.

Kotun shari’ar addinin musulunci dake zamanta a unguwar Jogana Kano, karkashin jagorancin mai shari’a, Kamalu Haruna, ta bayar da umarnin tsare mutanen da ake zargi da hada kai da yunkurin aikata tsafi. Wadanda ake tuhumar sun hada da, Yusuf Mahmud mazaunin Rano, Abdurraham Abbas mazaunin Kwasamgwami Gezawa da Sha’aibu Yawale Daganawa Bunkure da Abubakar Iliyasu […]

Read more

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa

Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa, ta fara horar da sabbin jami’anta daga Ƙananan Hukumomi 27 na jihar da kuma hedikwatar hukumar. Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Dauda Muhammad Hadejia ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa. Ya ce an fara horon a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, 2026, a sansanin NYSC da ke […]

Read more