Mujahid Wada Guringawa

Sojojin Sama Sun Yi Wa Yan Bindiga 400 Luguden Wuta A Zamfara

Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, harin da ta kai ta sama a karkashin rundunar ‘Operation Fansar Yamma’, a ranar Lahadi 10 ga watan Agusta, 2025, ta yi luguden wuta kan taron ‘yan bindiga 400 a lokacin da suke shirin kai hare-hare kan al’ummomi manoma a jihar Zamfara. Kakakin  sojojin, Air Cdre Ehimen Ejodame, […]

Read more

An gurfanar Da Waɗanda Ake Zargi Da Harin Cocin Owo

Mutum biyar da ake zargi da shirya harin bam a Coci Katolika ta Saint Francis da ke Owo, Jihar Ondo, a shekarar 2022, sun musanta tuhume-tuhume tara na ta’addanci da gwamnatin Tarayya ta shigar a kansu. An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya a ranar Litinin, inda ake […]

Read more

Za A Gina Layin Dogo Mai Amfani Da Lantarki A Kano

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta samar da titin dogo domin sufurin jirgin ƙasa a ƙwaryar birnin Kano da ke arewacin ƙasar, wanda zai laƙume naira triliyan 1 da rabi, a kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai Abubakar Kabir Abubakar ya bayyana. Jaridar DailyTrust ce ta ruwaito ɗan majalisar yana bayyana hakan ne a […]

Read more

Ƴan sanda Sun Saki Omoyele Sowore

Rundunar ƴansandan Najeriya ta saki ɗangwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi. Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasan ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya alaƙanta sakin nasa da nasarar kiraye-kiran sakin nasa da aka yi. Ya rubuta cewa, “Ƴansandan Najeriya sun amsa buƙatar ƴan gwagwarmaya. Yanzu haka […]

Read more