Wani Matashi Ya Daina Shan Kwaya Saboda Sauraren Shirye-shiryen MuhasaTVR

Mamalllakin tashohin Muhasa Radio da Talabijin, Muhammad Babandede OFR, OCM Spain, kuma tsohin Shugaban hukumar Shigi da Fici na Najeria, ya bayyana jin dadinsa kan yadda wani matashi ya kauracewa shan kayan maye saboda sauraren shirye-shiryen tashar Muhasa Radio.

A makon da muke ciki ne matashin ya kira waya don ya bayar da gudunmawarsa, a cikin shirin daga Titunan Kano, inda ya bayyana cewa sanadiyar sauraren gidan ne ya cire masa sha’awar shan kayan maye Saboda fadakarwar da ake yi Koda yaushe.

A cewar Matashin ya daina shan, Tabar Wiwi da taba Sigari Dama duk wani Abu da sanya shi maye, inda ya Muhasa addu’ar ci gaba samun nasara.

Muhammad Babanbade OFR OCM, ya ce a matsayin sa na mamalllakin tashohin, wannan babbar nasara ce agareshi da kuma dukkan ma’aikatansa.

” Na yi matukar Farin cikin jin cewa Saboda sauraren shirye-shirye da wani yake yi yau ya shiryu, ya zama mutumin da baya shan Kwaya” Muhammad Babandede’ ‘.

Ya kara da cewa wannan Babbar nasara ce shi da Kansa da kuma Daraktocin kamfanin da kuma ma’aikatansa musamman shugabannin gidan Radio.

Haka zalika ya godiya Janeral Manajar tashar da Mataimakan ta, Saboda wani ya shiryu bisa aiyuka nagari da suke yi, domin kwalliya ta biya kudin Sabulu.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya daukaka Muhasa, kuma masu saurare a ci gaba da jin tashar don amfana da ingantattun shirye-shirye kuma Allah yasa sauraran ya ci gaba da yin amfani mu gyara halayen mu nagari.

Post masu alaƙa

Ɗan Majalisar Tarayya Yaya Tongo ya rasu

DSS ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai a Kano

Farashin mai ya faɗi sosai saboda hasashen cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka