Shugaban Nijeriya Bola Tinubu Ya Ce Za Su Kawo Karshen Ta’addanci

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu.

Kalaman shugaban na zuwa ne a lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa ‘yanbindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna “yi wa Kiristoci kisan gilla”

Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a yau Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo “ta’addanci”.

“Duk da ƙalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da ƙawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance,” in ji shi.

“Ina tabbatar muku cewa za mu kawo ƙarshen ta’addanci. Abin da muka saka a gaba shi ne cigaba da ayyuka ido buɗe bisa manufarmu ta Sabunta Fata [Renewed Hope] domin gina Najeriya mai yalwa.”

Wannan karon farko da aka ga sugaban yana magana kan yaƙi da ta’addanci a fili tun bayan zargin da Trump ya yi kan Najeriya.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta sake jaddada haramcin hawan dawakai ko dabbobi da sunan “Da-ba.

Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi zuwa shekarar 2060.

Shugaba Tinubu ya lissafa nasarorin da ya samu a ƙasa da shekaru huɗu