Tinubu Ya Rantsar Da Sababbin Ministoci

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Bernard Mohammed Doro da Kingsley Tochukwu Udeh a matsayin ministoci.

Tun mako biyu da suka wuce ne majalisar tarayya ta amince da Mista Doro domin maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda daga jihar Filato, wanda ya zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai mulkin Najeriyar.

Sai a yau Alhamis ne kuma majalisar ta amince da naɗin Kingsley Tochukwu Udeh wanda zai maye gurbin Uche Nnaji daga jihar Enugu, wanda ya sauka daga muƙamin ministan kimiyya bayan zarge-zargen gabatar da shaidar karatu ta bogi.

Tinubu ya rantsar da ministocin ne jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa a fadar shugaban da ke Abuja.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin daji

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023