Victor Osimhen Ne Kan Gaba A Yawan Zura Kwallaye A Champions League

Ɗan wasan gaba na Nijeriya, Victor Osimhen, ya sha gaban fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland, Harry Kane, da Kylian Mbappé a yawan zura ƙwallaye a gasar Champions League ta bana.

Osimhen ya cimma wannan nasarar ce bayan ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Ajax a wasan zagaye na huɗu na gasar.

Wannan ya kai adadin ƙwallayensa zuwa shida, yayin da Haaland, Kane da Mbappé ke da ƙwallaye biyar-biyar kowannensu.

A watan da ya gabata, Osimhen ya kuma zura ƙwallaye uku a ragar Jamhuriyyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da ya ƙara masa farin jini a duniya.

Ɗan wasan da yanzu haka yake bugawa Galatasaray na Turkiyya, yana jan hankalin manyan kungiyoyi da dama a Turai, ciki har da Barcelona, wadda ke neman ƙwararren mai zura ƙwallaye domin cike gibin da ke cikin tawagarta.

 

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa