Babban Hafsan Sojin Kasa Na Najeriya Janar Taoreed Lagbaja Ya Rasu 

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da rasuwar Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.

Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya zama shugaban rundunar Sojin Kasa Najeriya a ranar 19 ga watan Yuni, 2023.

An tabbatar da rasuwar Janar Taoreed a ranar Talata bayan rashin lafiyar da ta tilasta fitar da dashi waje tun a kwanakin baya.

Allah Ya yi wa Janar Lagbaja rasuwa ne yana da shekaru 56, ya bar matarsa Mariya, da ’ya’ya biyu.

Hadimin Shugaban Kasa Kan Yada Labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana rasuwar Babban Hafsan Sojin yana mai mika ta’aziyyar Shugaba Bola Tinubu game da babban rashin da Najeriya ta yi.

Post masu alaƙa

NDLEA reshen jihar Kano ta ƙone haramtattun ƙwayoyi kilo dubu 12.

Sojojin Najeriya sun ceto ɗalibai da malamai 10 da aka sace a Borno

An kama wasu mutum 7 da ake zargin ƙusoshin Boko-Haram ne a filin jirgin Katsina