• Home  
  • Babban Layin Wutar Lantarkin Da Ke Kawo Wuta Arewa Ya Sake Ɗaukewa
- Babban Labari - Labarai

Babban Layin Wutar Lantarkin Da Ke Kawo Wuta Arewa Ya Sake Ɗaukewa

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukacin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na cikin duhu, da kuma wani yankin na Arewa ta Tsakiya. Mbah ta sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, inda har yanzu ake […]

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukacin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na cikin duhu, da kuma wani yankin na Arewa ta Tsakiya. Mbah ta sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, inda har yanzu ake gudanar da binciken inda matsalar take.

A makonnin baya dai matsalar ɗaukewar wutar lantarki yana neman zama ruwan dare a Najeriya. Cikin watanni biyu, wannan shine karo na shida da babban layin raba hasken wutar lantarkin yana ɗaukewa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai