Babbar Alkalin Jihar Kano, Dije Abdu-Aboki, ta rantsar da sabbin alkalan kotunan shari’a guda 30 da aka nada a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Baba Jibo-Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar a Kano.
Ya ce bikin rantsarwar wani muhimmin mataki ne na karfafa tsarin gudanar da shari’a a jihar.
A yayin bikin, Mai Shari’a Abdu-Aboki ta taya sabbin alkalan murna tare da bukatar su kasance masu tsoron Allah, tare da gudanar da aikinsu cikin gaskiya, adalci da rikon amana.
Ta kuma jaddada muhimmancin bin ka’idojin adalci, gaskiya da kuma doka a dukkan lamurran da za su gudanar.
A nasa jawabin, Babban Lauyan Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru-Maude, SAN, ya taya sabbin alkalan murna, inda ya bukace su da su kiyaye ka’idojin da’a a yayin gudanar da aikinsu.
Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kotuna na ci gaba da zama ginshikan adalci da zaman lafiya a cikin al’umma, tare da sake tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa bangaren shari’a.