Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu – Iran

Sojojin ruwa Iran sun ce mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai Amurka ta janye matakin rufe tashar ruwa Iran ɗin.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta yi jan kunnen daka “wani jargi ya tunkari tekun Gulf ko btekun Oman”.

Tace jirage da dama sun wuce ta mashigar daga jiya zuwa safiyar yau, amma da yammacin nan da ta fitar da sanarwar tace babu wanda zai sake wucewa har sai Amurka ta buɗe tashar jiragen ruwan Iran da ta toshe.

“Duk jirgin da ya tunkaro mashigar za mu ɗauke shi a matsayin na maƙiyanmu, kuma duk wanda ya karya doka za mu hare shi,” kamar yadda ta shaida a cikin sanarwar.

Post masu alaƙa

Ƴan sandan Kano za su ƙara ƙaimi wajen amsa kiran gaggawa – CP Bakori

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu