Barau Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Arewa A APC

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya zama ɗan takarar Sanatan Kano ta Arewa na jam’iyyar APC mai mulki.

An gudanar da taron tabbatar da takararsa a hedikwatar APC da ke Bichi, inda dubban magoya baya daga ƙananan hukumomi 13 na yankin suka halarta.

Bayan kammala taron, Barau ya gode wa magoya bayan jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna masa, tare da alƙawarin ci gaba da wakilci nagari.

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan jagorancinsa, yana mai cewa shugaban ƙasar na ƙoƙarin ciyar da Najeriya gaba.

Haka kuma ya yaba wa Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf kan ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa a jihar.

Barau ya buƙaci al’ummar Kano da su mara wa dukkan ’yan takarar APC baya a Zaɓen 2027, yana mai cewa kada su bari suka ko hayaniyar siyasa su karkatar da hankalinsu.

 

Post masu alaƙa

Zan mayar da tallafin man fetur idan na ci zaɓe – Atiku

Gwamnonin da ke shirin murɗe zaɓen 2027 za su sha mamaki — Kwankwaso

Zan tabbatar matatun man Najeriya sun koma aiki – Tinubu