Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku, ya ce gwamnati ta gaza kare ’yan Najeriya daga matsananciyar wahalar tattalin arziƙi.
Ya kuma ƙalubalanci iƙirarin Shugaba Tinubu cewa ana biyan albashi da fansho “a kan lokaci.
Ya bayyana cewa wasu ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sun koka kan jinkirin samun albashi, yayin da ’yan fansho ke ci gaba da yin zanga-zanga.
Atiku, ya kwatanta halin da Najeriya ke ciki da na Jamus, inda ya ce an rage harajin fetur da dizal da dala 0.17 kan kowace lita daga Oktoba zuwa Disamba domin rage wa jama’a matsin tattalin arziƙi.
“Idan farashin fetur ya tashi, kuɗin sufuri ma ya tashi. Idan kuɗin sufuri ya ƙaru, farashin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki su ma suna ƙaruwa,” in ji Atiku.
Ya bayar da shawarar a samar da tallafin da aka tsara musamman a fetur da ake tacewa a Najeriya, tare da ɗaukar matakai domin tabbatar da cewa tallafin ya rage farashin fetur.
“Ina bai wa duk wani ɗan Najeriya da aka tilasta masa zaɓar tsakanin ciyar da iyalinsa, biyan kuɗin sufuri ko biyan wata muhimmiyar buƙata cikin tsani, ina matuƙar ba da haƙuri. Ba ku cancanci fuskantar wannan wahala ba,” in ji shi.
Atiku ya ce rage farashin fetur na iya rage kuɗin sufuri da na kayan abinci.
Ya ce idan aka sauƙaƙa hakan zai bai wa magidanta damar samun ƙarin kuɗin da za su iya amfani da shi wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum.