Kotu ta soke nasarar ɗan takarar ADC a Majalisar Wakilai

Babbar Kotun Tarayya mai lamba biyu da ke Gombe ta soke zaɓen Bashir Abdullahi Gaddafi a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar ADC mai neman kujerar Akko a Majalisar Wakilan Tarayya a zaɓen 2027.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Vera E. Ibrahim, ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazabar cikin kwanaki 21.

Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin janye takardar shaidar nasarar zaɓen da aka bai wa Gaddafi nan take.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Adamu Hassan Kashere ya shigar, inda ya ƙalubalanci fitowar Gaddafi a matsayin ɗan takarar ADC, yana zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani a faɗin mazabu daban-daban na ƙaramar hukumar Akko ba.

Mai ƙarar ya kuma ƙalubalanci cancantar Gaddafi, bisa zargin cewa ma’aikacin gwamnati ne da ya shiga takarar fidda gwani ba tare da barin aikinsa a hukumance ba, yana ci gaba da karɓar albashinsa na wata-wata.

Sai dai, a cikin hukuncin da ta yanke, kotun ta ce mai ƙarar bai gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin cewa Gaddafi ya ci gaba da karɓar albashinsa yayin da yake takarar ba.

Kotun ta kuma amince cewa, Gaddafi ɗan  jam’iyyar ADC ne kuma yana da cancantar shiga takarar fidda gwani na jam’iyyar.

A yayin shari’ar, mai ƙarar ya nemi gabatar da wasu takardu domin ƙarfafa zarge-zargensa, amma an samu saɓani kan karɓar takardun a matsayin hujjoji a kotu.

Kashere ya shigar da ƙarar ne a kan Gaddafi, Jam’iyyar ADC da kuma INEC, yana ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen zaɓen Gaddafi a matsayin ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Post masu alaƙa

Tinubu zai fara yaƙin neman zaɓen shi daga Kaduna

Abin da ya sa jirgin soja ya yi saukar gaggawa a Benue – Sojoji

Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo