Gwamnatin jihar Bauchi Ta Gargaɗi Malamai Kan Kalaman Tunzura Jama’a

Sakataren gwamnatin jihar, malam Ibrahim Kashim ne ya yi wannan gargadin yayin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron kwamitin tsaro na jihar da suka gudanar a jiya litinin.

Ya kara da cewar, adai-dai lokacinda aka fito daga cikin mawuyacin hali na yakin neman zabe kuma abubuwa da dama sun faru bayan zaben da ke bukatar tsauraran matakan tsaro,

Saboda haka, gwamnati za ta tunkari duk wani mai wa’azi da ya yi kalaman da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin jama’a inda yace sun damu matika saboda ba batun Akida ba ne, ba batun siyasa ba ne, kawai batun tunzura maganganun da za su haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummarmu ne.

Kashim wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro, ya kara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Da yake nasa jawabi, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayyana cewa ana kokarin dakile ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar ta Bauci.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr