Birgediya Janar Kunle Nafiu Ya Zama Shugaban NYSC

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Kula da Hidimar Kasa (NYSC).

Kafin nadin nasa, Brigediya. Janar Nafiu shi ne Shugaban Ma’aikata na Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede. Haka kuma ya taba rike wannan mukami a lokacin marigayi Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Raised Abiodun Lagbaja.

Sabon Darakta Janar na NYSC, Dan asalin Ileogbo, Karamar Hukumar Aiyedire a Jihar Osun ne.

Nafiu, wanda nadinsa ya fara aiki nan take, zai maye gurbin Birgediya Janar Yushau Ahmed.

Post masu alaƙa

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa