Shugaba Tiani Ya Jagorancin Ɗaga Tutar Ƙungiyar AES 

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya jagorancin bikin daga sabuwar tutar kungiyar kasashen AES a hukumance wanda ya gudana a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Tiani ya jagoranci wannan biki ne a fadarsa da ke a babban birnin a gaban membobin gwamnatinsa.

A makonnin da suka gabata ne shugaban kungiyar AES kuma shugaban kasar Mali Janar Assimi Goïta ya gabatar da sabuwar tutar kungiyar ga ministocin kasashen uku da suka halarci wani taro a birnin Bamako.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa