Dan Sarkin Daura ya fito takarar dan Majalisar Wakilai

Muhammad Daha, ɗa ga Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Baure/Zango a zaɓen 2027. Daha, wanda ke rike da sarautar Danburam na Daura, ya ce matakin ya biyo bayan kiraye-kiraye  daga al’ummarsa da ke son ya wakilce su a Majalisar Tarayya. “Ina […]

Read more

Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi ya rasu.

Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, rasuwa a wani asibiti da ke ƙasar Masar, inda yake karɓar magani sakamakon fama da dogon rashin lafiya da ba a bayyana ba. Wani jami’in gwamnati a Birnin Kebbi ya ce an kai shi kasar waje domin jinya tun kafin fara azumin watan Ramadan […]

Read more

Gwamnonin Arewa sun yi alhinin rasuwar matar Farfesa Jega

Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun miƙa ta’aziyyarsu ga tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza. Hajiya Hadiza ta rasu ne a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarta bisa koyarwar addinin Musulunci bayan gudanar da sallar jana’iza a Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin […]

Read more

Kalaman Wike Na Barazanar Harbin Ɗan Jarida Sun Tayar Da Ƙura

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tsinci kansa a tsaka mai wuya, biyo bayan barazanar harbin ɗan jarida yayin da ake tsaka da gabatar da shiri a gidan talabijin. Wike ya yi wa fitaccen ɗan jaridar gidan talabijin na Channels, Seun Okinbaloye, barazanar harbi, lamarin da ya fusata ƙungiyoyin ’yan jarida da na kare […]

Read more

Ƙaramar ministar ƙwadagon Najeriya ta yi murabus

Ƙaramar Ministar kwadagon Najeriya Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus daga muƙaminta. Ta sanar da murabus ɗin nata ne a shafinta na X, inda ta miƙa godiyarta ga shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya bata dama ta yi aiki da gwamnatinsa. Ta bayyana ajiye muƙamin nata a matsayin matakin rufe wani gagarumin babi na rayuwarta a […]

Read more