Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin haƙar ma’adanai na Madaouela don sake fara aikin haƙar uranium, wani sabon mataki mai muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar.
A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a Yamai ranar Laraba, gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta ƙunshi biyan gwamnati dala miliyan 10 da farko, tare da samar da ayyukan yi kusan 1,000.
Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ne ya ruwaito yarjejeniyar.
Wannan mataki ya yi daidai da manufofin gwamnatin mulkin sojan Nijar na ƙara wa gwamnati iko kan albarkatun ma’adinai na ƙasar, tare da sake duba yarjejeniyoyin haƙar ma’adinai da kamfanonin ƙasashen waje.
Madaouela na daga cikin manyan wuraren da da arzikin uranium, inda aka kiyasta cewa yana ɗauke da kimanin tan 52,800 na uranium.
Kamfani dillancin labarai na AFP ya ce ana farfaɗo da aikin ne bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar da aka yi a baya da kamfanin GoviEx na Canada.
Wannan wani misali ne na yunƙurin mahukuntan Nijar na ƙara wa gwamnati iko da albarkatun ƙasar da kuma ƙarawa gwamnati kuɗaɗen shiga.