Labarai

Babban Labari Labarai

Yan Sanda Sun Tarwatsa Magoya Bayan Sanata Natasha Da Barkonon Tsohuwa

Ƴan sanda sun tarwatsa magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, waɗanda suka raka ta zuwa Majalisar Dattawa daga babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda suka watsa musu barkonon tsohuwa domin kora su. Magoya bayan sun yi tattaki ne domin raka sanatar zuwa majalisar domin ta koma bakin aikinta. Tun da farko, majalisar ta buɗe ofishin […]

Babban Labari Labarai

An Sace Dan Majalissar Dokokin Jihar Filato

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob. A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa […]

Babban Labari Labarai

Bayan Sallar La’asar Za A Yi Jana’izar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh

Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah […]

Babban Labari Labarai

Daurarru 68 Suka Ci Jarabawar NECO A Kano

Fursunoni 68 a Jihar Kano ne suka ci jarabawar kammala sakandaire ta NECO ta shekarar 2025, a cewar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen jihar. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, fursunonin sun ce wannan nasarar ta kasance abin farin ciki gare su inda suka bayyana cewa hakan zai zama wata babbar […]

Babban Labari Labarai

An Kama Yan Nijeriya 106 Da Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi A India

Hukumomi a Indiya sun tuhumi ‘yan Najeriya 106 da laifin safarar miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024 da ta gabata, kamar yadda jaridar Indian Express ta ruwaito. Rahoton ya ce ‘yan Najeriyar na cikin jimillar mutum 660 ne da rahoton shekara na hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya bayyana tare wasu daga ƙasashen Nepal (203), da Myanmar (25), […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai