Labarai

Babban Labari Labarai

Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya Ta Kaddamar Da Aiyukan Karfafa Asibitin Kware Na Sokoto

Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Zamantakewa ta Tarayya ta ƙaddamar da manyan ayyukan gine-gine guda 16 a Asibitin Neuropsychiatric na Tarayya da ke Kware, Jihar Sokoto. Wannan yana cikin shirye-shiryen inganta manyan cibiyoyin kiwon lafiya a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A wajen bikin ƙaddamarwa Ministan Jiha na Lafiya, Dokta Iziaq Adekunle […]

Babban Labari Labarai

Jam’iyyar PDP Ta Kafa Kwamitin Shirya Babban Taronta Na Kasa

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitin da zai shirya babban taron jam’iyyar a ƙarƙashin gwamman Adamawa Amadu Fintiri. PDP ta ce majalisar zartarwar ta amince da kafa wani ƙarin kwamitin da zai yi nazari a kan tsarin karɓa karɓan muƙamai a jam’iyyar gabanin babban taronta, a ƙarƙashin Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri. Jamiyyar ta ɗauki wannan […]

Babban Labari Labarai

Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ake Zargi Da Yiwa Matar Aure Kisan Gilla A Kano

  Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Sha’aibu Abdulkadir dan shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai dake kwaryar birnin jihar, bisa zargisa da halaka wata matar aure mai suna, Rumasa’u Haruna yar shekaru 22, a gidan auren ta dake unguwar  Farawa karamar hukumar Kumbotso ta jihar. Wanda ake zargin ya shiga […]

Babban Labari Labarai

Hukumar Samar Da Ruwa Ta Jihar Bauchi Ta Samu sabbin Kayan Aikin Magance Matsalar Karancin Ruwa

  Daga Mu’azu Hardawa Bauchi Ganin yadda ake fama da matsalar karancin ruwan Sha a cikin garin Bauchi da kewaye da kuma wasu kananan hukumomi na jihar Bauchi, Hukumar samar da ruwa ta jihar ta bayyana kokarin gwamnatin jihar Bauchi na samar da sabbin na’urorin samar da hasken rana domin tallafawa hasken lantarki na kasa […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai