Boko Haram Nada Banbanci Da Sauran Rikice-rikicen Da Najeriya Ke Fama Dasu-Jhonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ƙungiyar Boko Haram ta yi ƙarfin da ba a zato.

Jonathan, ya ce a wasu lokuta mayaƙan na Boko Haram suna da makaman da sojojin Najeriya basu da su.

Ya ce hakan ya tabbatar da cewa akwai hannun ƙasashen ƙetare a ƙungiyar.

Tsohon Shugaban ya ƙara da cewa matsalar Boko Haram ba ɗaya take da sauran rikice-rikice da Najeriya ta fuskanta ba, ya ce tana da tushen tsattsauran ra’ayi, da talauci, da wariya, da rashin adalci.

Shugaba Jonathan ya ce kawo ƙarshen Boko Haram na buƙatar haɗa matakan soja, da shugabanci nagari, da tallafi ga matasa, da inganta tsarin zamantakewa.

Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne a wurin bikin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum wanda tsohon shugaban hafsan sojoji, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta.

Jonathan ya yaba da littafin, ya kuma ce zai taimaka wa al’umma da shugabanni su fahimci rikicin Boko Haram sosai.

 

Post masu alaƙa

Babachir Lawal ya fita daga ADC

DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja

Tinubu ya ba da damar ɗaukar jami’an tsare dazuka 1,000 sakamakon garkuwa da ɗaliban jihar Oyo