Kasar Saudiyya ta kame mutane fiye da 17,600 da suka yi kokarin yin aikin hajjin bana ba bisa ka’ida ba
Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin bana Lt. Gen. Muhammad Al Bassami ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce, dagacikin waɗan da aka kamadɗin, 9,509 ne suka saɓa ka’idar bizar aiki da ta zaman ƙasar.