Dakarun gwamnatin kasar Sudan da ta RSF sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta saboda babbar sallah

A yau ne yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban rundunar dakarun RSF ya sanar za ta fara aiki domin bukukuwan babbar sallar Idi da za a fara ranar Laraba.

An bayar da sanarwar dakatar da rikicin ne a wani sakon murya da aka watsa a gidan talabijin, wanda shugaban kungiyar RSF, Muhammad Hamdan Dagalo, ya gabatar.

Ya ce matakin zai yi aiki ne a ranakun Talata da Laraba.

Janar Hemedti ya kuma yi Allah-wadai da cin zarafi da ake yi wa fararen hula – ciki har da wadanda sojojinsa ke yi.

Ana zargin kungiyar ta RSF da aikata laifukan cin zarafin mutane a Darfur.

Post masu alaƙa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Ebola ta ƙara bazuwa a DR Congo

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP