Labarai

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Adamawa, a matsayin wani giɓi […]

Read more

Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da wasu ziyarce-ziyarcen aiki zuwa Afirka ta Kudu, tare da cewa za ta kaurace wa duk wasu ayyukan majalisa da za su kasance a Afirka ta Kudu har zuwa wani lokaci. Matakin ya biyo bayan rahotannin kisan kai, hare-hare, tsoratarwa da lalata kadarorin da suka shafi ƴan Najeriya da sauran […]

Read more

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwato nau’in ƙwayoyi daban-daban har guda 5,916 da kuma kunshin tabar wiwi guda biyar. Kamen dai ya biyo bayan wasu samame na musamman da rundunar ta gudanar bisa bayanan sirri a wurare daban-daban na jihar, domin […]

Read more