Majalisar shura ta Tijjaniya ta yi addu’o’i kan kan matsalar tsaro da talauci a Najeriya
Majalisar Koli ta Darikar Tijjaniyya ta yi kira ga al’ummar Musulmin Najeriya da su mai da hankali wajen yin addu’o’in rokon Allah Ya warware matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassan kasar nan da kuma tsadar rayuwar da ake ciki yanzu haka.