An ayyana harshen Hausa cikin harsunan da za a fassara hudubar ranar Arafat
Mahukunta Masallatan Alfarma na kasar Saudiyya, sun sanya Hausa a cikin jerin harsuna 20 da za a yi amfani da su wajen fassara hudubar ranar Arafa ta bana. Daidai lokacin da mahajjata a sassan duniya suka fara aikin sauke farali na bana a kasar mai tsarki.