Shugaban Kungiyar Kwadago, NLC, Ya Nemi Gwamnatin Tarayya ta Hana Karin Kudin wutar Lantarki

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ƙi amincewa da shirin da ake yi na ƙara kuɗin wutar lantarki da kaso 40 ckin 100 nan da 1 ga Yulin 2023.

A sanarwar da ya fitar a Abuja, Kwamared Ajaero ya ce shirin na nuna halin ko-in-kula da rayuwar talakawan Najeriya.

Hukumar kula da farashin lantarki ta ƙasa ce ta amince da ƙarin kuɗin saboda tashin farashin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.

Sai dai shugaban na NLC ya buƙaci gwamnati ta hana wannan ƙarin kuɗin wutar.

A cewarsa “dole ne ayi la’akari da adadin wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke kawowa da kuma ƙarfin aljihun masu amfani da lantarki wurin biyan kuɗin.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa

Jami’ar Azare Za Ta Bai Wa Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Digirin Girmamawa