Labarai

Tinubu Ya Mayar Da Shugaban NTA Salihu Dembos

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon shugaban hukumar Talbijin na Ƙasar, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a 2023 – a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa […]

Read more

Masu Unguwanni 13 Sun Yi Murabus Daga Mukamansu A Jihar Kano.

Hakimin gundumar Jogana da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya amince da murabus ɗin wasu masu unguwanni su goma sha uku a ƙasarsa, waɗanda suka yi murabus don ƙashin kansu. ‎ ‎Abdulkadir Muhammad Balarabe, ya bayyana hakan ne a yayi zantawar sa da manema labarai ranar Talata 02 ga watan Satumban […]

Read more

An Ɓullo Da Sabuwar Manhajar Karatu A Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabuwar manhajar karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatun da za a fara a watan Satumbar bana a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da […]

Read more

Wike Ya Gindaya Wa PDP Sababbin Sharuɗa

Wasu ƴan jam’iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar da wani taro a daren jiya Litinin a Abuja, inda suka fitar da wasu sharuɗa da suka ce a cika kafin babban taron jam’iyyar, wanda za a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban bana a birnin […]

Read more

Muna Buƙatar Masu Fassara A Asibitoci : Kurame

Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. […]

Read more