Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar.
Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar Jamus, Johann wadephul, yana mai cewa Najeriya ƙasa ce mai bin doka da tsarin mulki, wadda ke tabbatar da cikakken ’yancin addini ga dukkan ’yan ƙasa.
“Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasa sun haramta cin zarafin addini, kuma suna tabbatar da damar kowane ɗan ƙasa ya gudanar da addininsa cikin walwala da kwanciyar hankali,” in ji shi
Ya ce babu yadda za a yi gwamnatin Najeriya ta goyi bayan duk wata hanya da za ta janyo cin zarafin mabiya wani addini, ko rikicin da zai haifar da tashin hankali irin wanda ya ruguza Sudan.
“Abin da muke so duniya ta fahimta shi ne, ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya. Ƙasarmu tana da yawan al’umma sama da miliyan 230, kuma ita ce ƙasa mafi girma ta dimokraɗiyya a Afirka,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ƙasashen waje za su bar ’yan Afirka su warware matsalolinsu da kansu, musamman Najeriya wadda ke cikin kwamitin tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, yaƙin da ake fafatawa a ƙasar Sudan da ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da raba wasu miliyoyi da matsugunansu cikin shekaru biyu da suka gabata, inda yanzu haka yaƙin ya bazu zuwa wasu yankunan ƙasar, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar wani mummunan bala’i na jin kai.
Barazanar Trump
A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Kiristocin Nijeriya suna fuskantar “barazanar gushewa” sakamakon kisan gillar da ake yi musu lamarin da ya ce shi ya sanya shi saka ƙasar a cikin ƙasashen da “ake matuƙar nuna damuwa a kansu.”
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Trump ya ɗauki matakin ne duk kuwa da cewa kwanakin baya mai ba shi shawara kan harkokin Afirka, Mossad Bullos, ya yi watsi da iƙirarin da ke cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.