Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jami’an yan sandan da suka samu Karin girma, su kasance masu riko da gaskiya kan amanar da aka dora mu su ,ta kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.
CP Bakori ya bayyana hakanne lokacin da yake likawa dakarun rundunar 29 karin girma, bisa umarnin babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, bayan hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa ta amince.
Mutane 2 sun samu Karin girma daga CSP zuwa mataimakan kwamishinan yan sanda wato ACP, sai mutane 21 daga mukamin SP zuwa CSP da kuma mutane 6 daga mukamin DSP zuwa SP.
Wadanda suka samu Karin girman sun hada da, ACP Gambo Chagwa Elijah, ACP Nasiru Yusuf, kakakin rundunar yan sandan Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, CSP Murtala Fagam baturen yan sandan Bichi, CSP Mohammed Abdulrahman Kanoma baturen yan sandan Bompai, CSP Ansar Muazu Marafa baturen yan sandan Nassarawa, CSP Musa Pindiga baturen yan sandan Mandawari, CSP Saleh Abubakar baturen yan sandan Doguwada CSP Jamilu Bala baturen yan sandan Rijiyar Zaki.
- Yan Sandan Jigawa Sun Kama Barayin Shanu Da Babura Da Dilolin Kwaya
- Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Unggogo Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Sauran sune, CSP Mohammed Acida baturen yan sandan Tsanyawa, CSP Safiyanu Mustafa baturen yan sandan Ganduje, CSP Mustafa Abubakar baturen yan sandan Kumbotso, CSP Yusuf Sunusi baturen yan sandan Shanono, CSP Adamu Gadama baturen yan sandan Takai, CSP Dansarai Jibrin baturen yan sandan Farm Centre, CSP Ibrahim Umar Baso, CSP Auwal Jumare, CSP Malami Abubakar, CSP Zubairu Abdulwahab, CSP Sani Bashir Umar, CSP Mukhtar Sani Baballe da kuma CSP Mohammed Sani da sauransu.
Kwamishinan yan sandan Kano, ya taya su murna tare da mika godiyarsa ga babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun da mataimakinsa mai kula da shiya ta daya zone one Kano bisa goyon baya da hadin kan da suke bawa rundunar.
Haka zalika kwamishinan yan sandan ya yi kira a gare su , su ci gaba da nuna kwarewa da yin abunda yakamata.