Gwamnan Osun Ya Buƙaci Tattaunawa Tsakanin Najeriya Da Amurka

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya yi kiran sabunta tattaunawar diplomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka, yayin da ake samun ƙaruwar nuna yatsa tsakanin ƙasashen biyu.

Cikin wata sanarwa da kakain gwamnan, Olawale Rasheed ya fita,, Gwamnan Adeleke ya buƙaci a tattauna kan barazanar da Shugaban Amurka ya yi a baya-bayan nan kan kai wa Najeriya hari.

Trump ya yi barazanar kai wa Najeriya hare-hare sakamakon abin da ya kira yawan kisan kiristoci a ƙasar.

Gwamnan ya yi kira a samar da wata hanyar lalama domin samo bakin zaren tsakanin ƙasashen biyu.

“Ina kira ga fadar shugaban Amurka ta tallafa wa Najeriya wajen aiwatar da sabbin dabarun tsaro na zamani”, in ji shi.

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.