Labarai

Harin Lassa: Zulum ya tura tawaga ta musamman yankin, an rufe wasu makarantu

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tura tawaga ta musamman zuwa garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba bayan harin da ’yan ta’adda suka kai makarantar sakandaren gwamnati ta Lassa. Tawagar ta samu jagorancin Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-Ƙirƙire, Injiniya Lawan Abba Wakilbe. Haka kuma ta haɗa da Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi, Samaila […]

Read more

NDLEA reshen jihar Kano ta ƙone haramtattun ƙwayoyi kilo dubu 12.

Hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta ƙone haramtattun ƙwayoyi fiye da kilo dubu goma sha biyu.Kwamandan hukumar na jihar Kano, Dahiru Lawan Yahya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar ƙone miyagun ƙwayoyin, a yankin hawan Kalebawa dake ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa Kano. Kwamandan NDLEA na Kano, […]

Read more

KACRAN ya ti watsi da ƙirƙiro ƴansandan jihohi a Najeriya

Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kullen Allah ta yi kira ga hukumomin Najeriya su dakatar da batun ƙirƙiro ƴansandan jihohi a faɗin ƙasar. Yayin tattaunawarsa da BBC, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mohammed Khalil Bello ya ce shirin ba shi da wata fa’ida illa haifar da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar. Ƙungiyar makiyayan ta bayyana fargabar cewa […]

Read more