Babban Labari

Yajin Aiki: NARD Za Ta Yi Zanga-Zangar Lumana A Zariya

Ƙungiyar Likitoci Masu Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, ta sanar da aniyarta ta shiga yajin aiki na ƙasa da aka shirya fara wa a ranar 12 ga watan Janairu, 2027. Wannan ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta cimma […]

Read more

Na Gamsu Ana Kashe Musulmai A Najeriya — Trump

A karon farko tun bayan da ya fara magana kan matsalar tsaro a Najeriya, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa ana kashe Musulmai a ƙasar. A baya, Trump ya sha bayyana cewa hare-haren da ake kai wa a Najeriya sun fi shafar Kiristoci kaɗai, duk da cewa rahotannin sun nuna cewar mutane daga kowane […]

Read more

Ƙungiyar matasan ƙabilar Ijaw ta buƙaci Tinubu ya sauke Wike

Ƙungiyar matasan al’ummar ƙabilar Ijaw ta yi kira da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauke Nyesom Wike daga ministan Abuja. Shugaban ƙungiyar, Alaye Theophilus ne ya bayyana kiran yayin wani jawabi da yake yi wa manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers. Mista Theophilus ya kuma yi allah wadai game da yunƙurin ƴan majalisar […]

Read more

Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban NMDPRA zuwa EFCC

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur ta Najeriya, NMDPR, Farouk Ahmed, gaban EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa. Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito wata sanarwa daga kamfanin Dangoten, cewa shugaban kamfanin ya shigar da […]

Read more

Kotu ta bayar da umarnin a kama jami’in DSS Kirista Ifeanyi Festus, bisa zargin sace yarinya musulma da cin zarafinta.

Wata kotun majistiri dake zamanta a Hadejia jihar Jigawa ta bayar da umarnin kamo wani jami’in hukumar tsaron farin kaya, DSS, mai suna Ifeanyi Festus, bisa zarginsa da sace karamar yarinya da tursasa mata sauya addininta zuwa kiistanci tare da cin zarafinta ta hanyar lalata. A cewar kotun, ana zargin jami’in da sace Walida Sani, […]

Read more

Gobara ta ƙone dukiyar N15m a Gusau

Gobara ta ƙone dukiya ta kimanin Naira miliyan 15 wadda ta tashi a wata ma’adanar kayan ado da ke unguwar Barakallahu a birnin Gusau na Jihar Zamfara. Wani ganau, Sambo Balarabe, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 8 na dare, bayan wani direban babur da ke wucewa ya hango hayaƙi na tashi […]

Read more

Majalisar Dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, lamarin da ya haddasa ruɗani a siyasar jihar. A zaman majalisar na ranar Alhamis, da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban Masu Rinjaye, Major Jack, ya karanta takardar zargin da ake yi wa gwamnan bisa aikata manyan laifuka. Ya […]

Read more